Fadar Shugaban Kasa tace Babu wata Jiha da aka bawa izinin sayan makami mai sarrafa kansa

Guns 750x430 1
Guns 750x430 1

Gwamnatin Tarayya ta ce babu wata Jiha a Kasar nan da aka ba wa izinin siyan makamai masu sarrafa kansu don inganta harkokin tsaronta.

Mai taimakawa shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Malam Garba Shehu, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa daya fitar ranar Talata a Abuja.

Garba Shehu, ya yi watsi da rahotannin dake cewa an baiwa gwamnatin jihar Katsina lasisin sayowa da sarrafa makamai masu sarrafa kansu.

A cewarsa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sha bayyanawa karara cewa babu wanda aka yarda ya dauki AK-47 ko wani makami ba bisa ka’ida ba, kuma duk Wanda ke da shi dole ne ya mika shi.

Shehu ya tabbatar da cewa fadar shugaban kasa ta yaba da yadda jahohin kasar ke yin kokari a harkokin tsaro.

Don haka ya yabawa gwamnatocin jihohi bisa yadda suke taimakawa jami’an tsaro a ci gaba da yaki da ‘yan ta’adda da sauran miyagun laifuka a fadin kasar nan.

Shehu ya lura cewa kokarin hadin gwiwar gwamnatocin jihohi da hukumomi wajen tabbatar da doka yana ci gaba da samun sakamako mai kyau.

Wadda hakan, a cewarsa, yana dakile yunkurin ‘yan ta’adda na yin barna da ayyukan ta’addanci ga al’umma.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here