EFCC ta cafke malamin addini da wasu mutane da dama ƴan Yahoo a jihar Kwara

EFCC, kwato, naira, biliyan, Olukoyede
Shugaban hukumar EFCC ta Najeriya Mista Ola Olukoyede, ya ce a cikin kwana 100, ofishinsa ya samu ƙorafe-ƙorafe 5,000 da suka danganci almundahana, kuma ya...

Jami’an hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasa (EFCC) sun yi babban kamu a birni Ilorin na jihar Kwara. Jami’an na EFCC a ranar Alhamis sun samu nasarar cafke wasu mutum 28 da ake zargi da aikata laifukan damfarar yanar gizo wato Yahoo-Yahoo.

Cafke ɓata garin wanda aka samu nasarar gudanar da shi a unguwar Mandate, cikin birnin Ilorin, ya biyo bayan samun bayanan sirri da akayi kan ayyukan da ƴan damfarar suke aikatawa a unguwar.

Binciken farko da aka gudanar ya bayyana cewa daga cikin ɓata garin da aka cafke akwai wani malami, tagwaye, ɗalibai shida na makarantar gaba da sakandire daban-daban, mai haƙar ma’adanai da dai sauran su.

Sunayen waɗanda ake zargin sune Toheeb Albarka (malami); Lambe Kehinde da Lambe Taye; Francis Stephen; Olabode Yusuf, da Musbaudeen Akorede. Masu yin karatu a makarantun gaba da sakandire daga cikin su sune: Moshood Okunola; Kayode Aderemi; Ayobami Olorunfemi; Paul Ayomide; Agboola Marvellous, da Adebisi Olatunde. Sauran sun haɗa da Olaleye Solomon (mai haƙar ma’adanai); Akinade Samuel; Damilola Shagaya; Muhammed Awal; Adam Mubaraq; Ogundiran Nathaniel; Jamiu Ishola; Dauda Tunde; Abdullahi Sikiru; Kasali Adegoke; Jordan Adeyinka, da kuma direba, Ojeniyi Boluwatife. Ragowar ƴan waɗanda ake zargi da damfanar sune, Adedamola Samson; Olarewaju Taofeek; Adewale Oloro, da Omogbolahan Ibrahim. Kayayyakin da aka kwato daga hannun su sun haɗa motoci tsala-tsala guda 10, kwamfutoci daban-daban, wayoyin hannu, firinta da dai sauran su.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here