Dogayen layukan mai: Kada ku tsorata, Muna da wadataccen mai a runbunan ajiya – NNPC Ltd

fuelques
fuelques

Kamfanin hada hadar man fetur na kasa ya jaddada da jama’a cewa kamfanin na da isasshen albarkatun man fetur don haka bai kamata jama’a su yita gaggawar siyan man a tsorace ba.

Kamfanin a cikin wata sanarwa da ya fitar ta hannun Babban Manajan Rukunin Rukunin Hulda da Jama’a na Kamfanin Garba Muhammad, ya ce ahalin da ake ciki a halin yanzu ana samun dogayen layuka a wasu sassan Abuja da kewaye wanda ya samo asali sakamakon tsaikon zuwa motocin dako.

Rahotanni sun nuna cewa hakan nazuwa ne sakamakon ambaliyar ruwa da ta mamaye wasu sassan babbar hanyar da ta ratsa birnin Lokoja a jihar Kogi.

Rahotannin sun kara dacewa matsalar ta samo asali ne awani sashi na hanyar dake dab da babbar hanyar Badegi-Agaie a jihar Neja.

“Saboda haka, motoci, musamman tankunan mai, na neman wasu hanyoyin da za su kai ga inda dora musu kayan.

“Kamfanin NNPC na aiki tukuru, tare da haɗin gwiwar hukumomin gwamnati, don buɗe wannan babbar hanyar.

“Muna kira ga jama’a da su kwantar da hankula kuma kada su firgita wajan siyan kayayyakin man a tsorace,” in ji shi.

A cewarsa, halin da ake ciki yanzu na wucin gadi ne kuma ba shi da alaka da karancin Motoci kamar yadda kamfanin ke da isasshen kayan aiki(Man Fetur) na tsawon kwanaki talatin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here