Dalilin Da Yasa Zan Goyi Bayan Tinubu Bayan Nabar Mulki – Gwamna Ortom.ß

Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom ya yi fatali da rade radin da ake masa na yiwuwar sauya sheka zuwa jam’iyyar APC bayan ya bar mulki.

Gwamnan mai barin gado ya sha alwashin goyon bayan zababben shugaban kasa, Bola Tinubu duk da matsayin sa na mamba a jam’iyyar PDP.

Da yake magana a shirin safe na gidan talabijin na Arise, gwamnan ya ce zai ci gaba da tabbatar yin adalci a tsakanin ‘yan Najeriya.

Gwamna Ortom ya ce ya yi fafutuka dan ganin kudancin Najeriya ya sami shugabancin kasar saboda yana son a yi raba daidai da adalci.

A cewarsa: “Wannan ba ya kan matsaya, ina nan a PDP, kuma na yi fafutuka ganin shugaban kasa ya fito daga Kudancin kasar, wanda Tinubu da Obi suke ciki.

“Sauya sheka zuwa wata jam’iyyar ba ya gaba na” Ortom.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here