
Tsohon shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya ce da gangan yaki bada takardar shaidar kammala karatun sakandirensa lokacin takarar zaben shekarar 2015 duk da cece-kucen da jama’a suka yi tayi a fadin kasar.
Buhari yace ya gano inda ya aje takardar shaidar kammala karatun sakandiren a shekarar 2018, amma yayi kememe wajen gabatar da shi domin hana masu zargin sa samun damar ci gaba da tsokaci a kai.
Tsohon shugaban yace abune da bai zai yiwu ba ya tafi kasar India yin karatu a cibiyar horar da kananan hafsoshin sojin kasar a shekarar 1973 da kuma cibiyar horar da dabarun yaki ta Amurka idan bai mallaki takardar shaidar da ake magana a kai ba.
Karanta wannan: Gwamna Aiyedatiwa ya nada tsohon ma’aikacin Hukumar NASS mataimakinsa
Buhari yace a lokacin da suka yi makaranta yana da wahala a samu masu aikata laifuffukan satar jarabawa ko kuma mallakar takardun bogi.
Tsohon shugaban yace shi da abokansa da suka yi karatu na shekaru 9 a firamare da sakandare, cikin su harda Janar Shehu Musa Yar’Adua sanda suka rubuta jarabawa kafin samun damar shiga makarantar soji.
Buhari yace sanda aka gwada su a fannin Turanci da Lissafi da kuma bangaren ilimin bai daya.
Wadannan bayanai na tsohon shugaban kasar na kunshe ne a cikin sabon littafin da mai bashi shawara a kan harkokin yada labarai Femi Adeshina ya wallafa aka kuma kaddamar a makon jiya.












































