Dakatar da Motocin dakon Mai: Masu tankar mai za su yi Asarar Nairar Biliyan 300 – NARTO

Tanker explosion new

Kungiyar masu safarar motoci ta kasa (NARTO), ta bayyana fargaba kan shirin gwamnatin tarayya na haramtawa motocin dakon man fetur guda 60,000, biyo bayan karuwar hadurran da suke faruwa da tankokin mai.

Shugaban NARTO, Yusuf Othman a wata hira da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN a Abuja ranar Lahadi, ya ce irin wannan matakin zai janyo asarar jarin Naira biliyan 300 ga masu motocin dakon mai.

NAN a rahotonta, ta ce gwamnatin tarayya, ta hannun hukumar kula da man fetur ta kasa (NMDPRA) na shirin sanya dokar hana jigilar motocin man fetur guda 60,000, saboda hadurra da ke haifar mutuwar mutane a kasar nan.

Karin karatu: Matatar man Dangote ta rage farashin man fetur zuwa Naira 890 a kowace lita

Hukumar ta NMDPRA ta ba da shawarar kayyade karfin tankunan mai zuwa iyakar lita 45,000 don rage hadurra sakamakon fashewarsu.

Baya ga tantance adadin nauyin da tankunan za su dauka, hukumar ta NMDPRA ta sanya wasu matakan tsaro, da suka hada da sanya na’urorin tsaro a cikin manyan motocin dakon mai, da wayar da kan jama’a da taron masu ruwa da tsaki na yau da kullum, da sauransu.

Ya ce manyan motoci 2,000 masu karfin lita 60,000 kowannensu ya kai Naira miliyan 150, wanda adadinsu ya kai N300b zuba jari a harkar safarar man fetur a fadin kasar nan.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here