Da zafi-zafi: Sojoji sun karɓe mulki a Jamhuriyar Benin

Benin Republic Coup

Tawagar sojoji a sun bayyana a gidan talabijin na ƙasa na Jamhuriyar Benin a safiyar Lahadi, inda suka sanar da rushe gwamnatin ƙasar tare da tsige shugaban ƙasa Patrice Talon.

Sojojin sun kira kansu da Kwamitin Sojoji na Gyaran Gida, tare da bayyana cewa sun cire shugaban ƙasa da dukkan sauran cibiyoyin gwamnati.

Rahotanni sun nuna cewa tarzomar ta fara ne da wani hari da aka kai gidan shugaban ƙasa da ke Porto-Novo da misalin farkon asuba, wanda Laftanar Kanar Pascal Tigri ya jagoranta tare da dakarun da ke goyon bayansa.

Daga bisani dakarun sun karɓi ikon gidan talabijin na ƙasa, inda suka karanta sanarwar cewa sun ɗauki nauyin jagorancin ƙasar domin dawo da tsari da kwanciyar hankali.

Har yanzu ba a tabbatar da matsayin shugaban ƙasa Patrice Talon ba, domin dakarun sun ci gaba da tsare muhimman wurare na gwamnati.

Rahotannin da ke fitowa daga ƙasar sun nuna cewa jama’a na cikin fargaba yayin da ake ƙara samun motsin sojoji a manyan tituna na Porto-Novo.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here