Kungiyar Makiyaya ta miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria MACBAN, ta ce za ta gina matsugunai ga ‘ya’yanta masu rauni da ke rasa wuraren zama saboda sauyin yanayi.
Zababben shugaban kungiyar na kasa, Alhaji Baba Othman-Ngelzarma ne ya bayyana hakan a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Najeriya a karshen mako a Abuja.
Ya ce: “Za mu yi amfani da damar da ake samu musamman shirin sauyin yanayi da aka rattabawa hannu a yayin taron sauyin yanayi na Masar COP27.
Kungiyar ta bayyana wasu daga cikin illolin sauyin yanayi da ke shafar mambobinta da suka hada da gurbacewar muhalli, da kare wuraren kiwo da albarkatun ruwa, saurin kwararowar hamada da kuma yin hijira.
“Kuma ta wannan hanyar ne za mu ci gaba da yin kira ga jihohi da gwamnatin tarayya da su fito da tsarin sasantawa wanda zai dace da irin na makiyayan da muke da su a kasar nan.”
Othman-Ngelzarma ya ce kungiyar ta shirya yin hadin gwiwa da kungiyoyi masu zaman kansu na cikin gida da na waje, da kuma abokan huldar cigaba don karfafa hanyoyin inganta tsarin kiwo da samun damammaki daga makiyaya.
“Har ila yau, burinmu shine na yakar satar dukiyar jama’a, hada kai da kuma nuna wariya.













































