Shugaban kasa Bola Tinubu ya kaddamar da motocin haya guda 107 da suka hada da masu amfani da wutar lantarki guda 50 da gwamnatin Borno ta saya.
Da yake jawabi a wajen bikin, Tinubu ya yabawa Gwamna Zulum bisa hangen nesa da kuma manufofinsa na ciyar da al’umma gaba.
Ya bayyana cewa gwamnatin tarayya na shirin kafa wata masana’anta da zata samar da ayyukan yi da kuma saukaka harkokin sufuri.
Karanta wannan:Shahararren Mawakin Yarabawa, Olanrewaju Adepoju, Ya Rasu

Tun da farko Gwamna Zulum ya ce ya samu kwarin giwar wannan aiki ne biyo bayan umarnin da shugaban kasa ya ba gwamnoni bayan cire tallafin mai.

Yace samar da motocin haya guda 50 masu amfani da lantarki su ne na kashin farko a Najeriya kuma ya yi dai-dai da sauyin yanayi da ake fuskanta.

Kamfanin dillancin labarai NAN ya rawaito cewa motocin da shugaban kasar ya kaddamar sun hada da motocin haya masu amfani da wutar lantarki guda 50, da bas-bas 35 sai Hummer guda 12, da manyan motocin alfarma guda 10.
NAN ya kuma rawaito cewa shugaban kasar wanda ya kai ziyarar aiki ta farko a jihar, ya ziyarci Shehun Borno, Abubakar El-Kanemi.













































