Daga: Aminu Halilu Tudun Wada
Dan wasan jihar Kano mai bukata ta musamman, na ajin wasan daga nauyi (Para Weight lifting) Ahmad Yahaya, ya ce bashi da wani buri illa ya zama Zakaran wasan Olympic.
Ya bayyana hakan ne Jim kadan bayan karbar lambar Tagulla, mataki na uku a wasan Ajin daga nauyi na gasar masu bukata ta musamman karo na 2 dake gudana a Abuja.
Karanta wannan:Cikakkun sunaye: Nijeriya na da alƙalan wasa 29 na FIFA
Ahmad Yahaya ya lashe lambar kyautar ne, bayan fafatawa da abokan karawar sa daga jihohin Osun, Ondo da Oyo, Delta da Rivers.
Matashin yace duk da kalubalen da aka samu na rashin kudaden gudanarwa da kuma kayayyakin motsa jiki kafin gasar, hakan bai sa ya karaya ba sai ma karin karsashi domin ganin ya samu nasara tare da fito da sunan jihar Kano a Fannin wasan.














































