Bashin Naira biliyan 307 mu ka gada daga gwamnatin Lalong – Gwamnan Plateau

358644031 606129471691749 2721363008608619014 n
358644031 606129471691749 2721363008608619014 n

Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Plateau ya ce gwamnatinsa ta gaji bashin Naira biliyan 307 daga gwamnatin da ta gabata ta Simon Lalong.

Gwamnan ya bayyana hakan ne jim kadan bayan karbar rahoton kwamitocin da ke kula da tsarin mika mulki da tsare-tsare na jihar a jiya Litinin a Jos.

Kwamitocin biyu sun kasance karkashin jagorancin Farfesa Ganyir Lombin.

Gwamnan ya bayyana aniyar sa na ganin jihar ta kai ga gaci, duk da dimbin bashin da ake bin ta.

Mutfwang musamman ya bayyana shirinsa na tunkarar kalubalen tsaro a jihar.

“A lokacin yakin neman zabe, mun zaci cewa bashin da ake bin mu ya kai kusan Naira biliyan 200; jin cewa Naira biliyan 307 abu ne mai ban tsoro da damuwa.

“Amma, da yardar Ubangiji za mu shawo kan waɗannan ƙalubalen da muke fuskanta a jihar,” in ji gwamnan.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here