Jam’iyyar APC ta umarci dukkan masu kula da rajistar membobinta na jihohi da su tabbatar an yi rajistar kowane memba ba tare da an bar kowa a baya ba, tare da gargaɗin cewa duk wanda ya gaza cika wannan umarni za a maye gurbinsa.
Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya bayar da wannan umarni ne ta cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai da dabarun sadarwa, Abimbola Tooki, ya fitar bayan ganawa da masu kula da rajistar jihohi a Abuja.
Sanarwar ta bayyana cewa aikin rajistar membobinta ta hanyar na’ura ya fara aiki kuma an tsara kammala shi cikin wa’adin da aka ware.
Shugaban jam’iyyar ya bayyana cewa wannan tsari muhimmin gyara ne na siyasa ga APC domin ƙarfafa sahihanci, tattarawa, da ƙarfinta a zaɓe.
Yilwatda ya bayyana cewa matsayin mai kula da rajista ba na alfarma ba ne, illa babban nauyi ne da ke da alaƙa kai tsaye da ƙarfin jam’iyyar a matakan jiha, sanata, mazabu, ƙananan hukumomi da ma gundumomi, yana mai nuna cewa nasarar jam’iyya a zaɓe tana farawa ne daga waɗannan matakai.
Shugaban jam’iyyar ya yi gargaɗi kan yanayin da jihohi ke da’awar yawan membobi amma sakamakon ƙuri’unsu ya kasance ƙasa, inda ya ce dole adadin mambobi ya dace da ƙarfinsu a zaɓe, tare da cewa dukkan mambobin kwamitin zartarwa na jihohi da ba su yi rajista ba za a cire su daga muƙamansu.
Ya kuma ja hankalin shugabannin jam’iyyar na jihohi da su ba da cikakken goyon baya ga aikin rajistar, yana mai haramta duk wani yunƙuri na hana ko ware mambobi daga yin rajista, tare da umarnin amfani da wayoyin Android inda babu allunan aiki domin kauce wa jinkiri.
Yilwatda ya bayyana cewa rajistar ta hanyar na’ura za ta samar wa APC cikakken kundin bayanan membobi mai sahihanci da za a iya tantancewa, wanda zai ƙarfafa dimokuraɗiyyar cikin gida, inganta shirin kamfe da rage maguɗi.
Tuni dai masu kula da aikin rajistar suka yi alƙawarin kammala aikin cikin wa’adin da aka tsara.
NAN












































