Bayan wani juyin-juya-hali, gwamnatin Jihar Kano da masu filaye a unguwar Dangoro da ke Kumbotso sun cimma matsaya kan rikicin filayen da ake takaddama a kansu.
Wannan ya biyo bayan zaman da suka yi da Kwamishinan Ƙasa, Abduljabbar Umar Garko, a ranar 27 ga Nuwamba.
Rikicin ya samo asali ne bayan da gwamnati ta bayyana niyyar mayar da kasuwar ’Yan Lemo da ta kayan marmari ta Yankaba zuwa Dangoro, abin da ya tayar da fargaba ga al’umma cewa za a kwace filayensu.
A ranar Asabar kuwa, shugabannin masu filayen suka taru domin sanar da mambobinsu sakamakon ganawar da suka yi da kwamishina, yayin da ake shirin fara aikin gwamnati a mako mai zuwa.
Shugaban ƙungiyar masu filayen, Alhaji Gambo Saminu Adamu, ya ce sun kira taron ne domin kwantar da hankalin jama’a cewa abin da suka amince da gwamnati za a aiwatar cikin adalci.
Ya ce sun yarda da tsarin rabon 50-50, inda gwamnati za ta ɗauki rabin fili, rabin kuma ya rage ga mai fili.
Ya kuma gode wa gwamnati tare da yin kira da a kara haƙuri.
Wani daga cikin shugabannin, Sunusi Haruna, ya ce sun wayar da kan jama’a game da dalilan amincewa da kudurin gwamnati tare da gargadin cewa duk wani abu da ya saba da yarjejeniyar ba za su karɓa ba.
A nasa bangaren, Jami’u Akilu ya ce suna bukatar a tsaya tsayin daka kan adalci, tare da tabbatar da cewa kasuwannin da za a kawo yankin za su amfanar da ’yan ƙasa ba wasu na waje ba.
Duk da haka, al’ummar yankin sun nuna fatan alheri, inda suka ce suna maraba da cigaban, matuƙar za a kare musu hakkinsu.
A baya, gwamnatin jihar Kano ta bayyana tsarin da za ta bi wajen amfani da filayen da ake rikici a kansu a Dangoro, inda ta tanadi tsarin rabon 50-50.
Misali, idan fili zai iya ɗaukar shaguna 10, gwamnati za ta samu biyar, mai filin kuma ya mallaki sauran biyar—domin daidaita ci gaba da kare haƙƙin masu filaye.













































