Ministan Sufuri kuma mai neman takarar shugabancin Najeeriya karkashin Jam’iyyar APC, Rotimi Amaechi, yace zai yi murabus a ranar Litinin din nan.
Wannan na zuwa ne bayan umarnin da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayar cewa wanda ke rike da mukamin Gwamnati kuma yake sha’awar tsayawa takara a zaben shekarar 2023, ya zama wajibi ya sauka daga mukamin sa.
Amaechi ya bayyana hakan ne ranar Lahadi Yayin da yake ganawa da wakilan Jam’iyyar masu zaben Dan takara a Jihar Kaduna.
Ministan ya kuma bayyana ya kuma bayyana godiyarsa bisa alamun goyon baya da yake gani a kudurinsa na hidimtawa Kasar.
Yayin da yake bayyana aniyarsa ta ajiye aikin Ministan Sufurin tarayyar Najeriya a ranar Litinin din nan 16 ga watan Mayu, Amaechi yace yana daga cikin Masu neman tsayawa takarar shugabancin Kasar masu Karancin Shekaru.
Ya kuma bukaci sauran masu neman tsayawa takarar dake da manyan shekaru cewa su bar batun takara su koma gida domin su huta tare da hidimtawa Iyalansu.
Kazalika yace ya shugabanci jihar da a lokacin da ya hau karagar mulkin take fama da matsanancin rashin tsaro, amma bisa jajurcewa da sadaukarwa sai da ya magance matsalar, dogaro da wancan kokari ne ma ya sanya yake da kwarin gwiwar gina sabuwar Najeriya.
Da yake tarbar Ministan a madadin wakilan Jam’iyyar na Jihar Kaduna Gwamnan jihar Malam Nasir El-Rufai, ya bayyana Amaechi a matsayin Aboki kuma mutumin da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ke da kwarin gwiwa a kan shi wanda ya hidimtawa Jam’iyyar tsawon lokaci.













































