Sanata mai wakiltan Kogi ta tsakiya a majalisar dattawa, Natasha Akpoti-Uduaghan, ta bayyana asalin rikicin da ya shiga tsakaninta da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, inda ta ce ya bukaci yayi lalata da ita.
Sanata Natasha wadda ta auri wani hamshakin attajirin dan kasuwa haifaffen jihar Delta, ta bayyana hakan ne a cikin shirin karin kumallo na gidan talabijin na Arise News Channel mai suna ‘The Morning Show’ da safiyar Juma’a.
Idan za a iya tunawa an samu wani rikici tsakanin Natasha da Akpabio a zauren majalisar dattijai a makon da ya gabata kan sauyin wurin zama.
A farkon makon nan ne Majalisar Dattawa ta mika batun ga kwamitinta ɗa’a da ladabtarwa har ma da sauraron kararrakin jama’a domin gudanar da bincike.
Karin labari: Zargin ɓata suna: Sanata Natasha ta maka Akpabio a kotu, tare da nema Naira biliyan 100.3 na shigar da ƙara
Sai dai da take magana a shirin talabijin kai tsaye, Sanatan ta Kogi ta tsakiya ta ce lamarin ya fara ne a watan Disambar 2023 a wata ziyarar aiki da ta kai jihar Akwa Ibom yankin su Akpabio, ta yi zargin cewa shugaban majalisar dattawan ya yi amfani da wannan damar wajen gayyatar ta da mijinta domin su ziyarci gidansa da ke Uyo babban birnin jihar.
Natasha ta ce a lokacin da Akpabio yake zagayawa da su a katafaren ginin gidansa, ya shaida mata cewa zai iya samar musu da fili a cikin gidan domin jin dadinsu.
Natasha ta kuma tuno wani abin da ya faru a majalisar Dattawa a lokacin da ta bukaci a gabatar da kudiri a kan Ajaokuta, wanda ke cikin yankinta, amma Akpabio yaki saurara. Ta ce daga baya ‘yan uwanta Sanatoci suka ba ta shawarar ta gana da shi a kebe domin daidaita al’amura a kan kudirin
Natasha ta ce Akpabio ya shaida mata cewa za ta samu damar shigar da ƙudirin na Ajaokuta ne kawai idan ta shirya amincewa da shi.
Sanata Natasha ta kuma yi zargin cewa wani shugaba a majalisar Dattawa, Sanata Opeyemi Bamidele, ya taba kiranta da tsakar dare domin ya yi mata barazana a kwanan baya kan rikicin da ya faru da Akpabio, inda ta ce ‘yan majalisar Ekiti ta tsakiya sun yi gargadin cewa ‘idan Akpabio ya sauka’ ita ma za ta sauka