Sama da mutane 25 ne suka mutu sakamakon bulkar ciwon mashako a jihar Kano.
Jaridar Solacebase ta tattaro cewa tun a ranar Juma’a 13 ga watan Janairun 2023 ne cutar wadda ke kashe kananan yara wacce aka gano ta a shekarar 2022, ta sake bulla a Kano, inda yanzu haka ake bawa wadanda suka kamu da ita kulawar gaggawa a asbitin kwararru na Murtala Muhammed da kuma asibitin koyarwa na Aminu Kano, a jihar Kano.
Kwararun likitoci sun bayyana cewa wannan cutar da ke harbar hanci da makogaro za’a iya samun kariya daga kamuwa da ita ta hanyar amfani da rigakafi wato (vaccine.)













































