Masu garkuwa da mutane da suka sace manoma biyu a Osun, Samuel Oyedotun da Tobiloba Fashola sun sake su tare da wanda ya tafi biyan kudin fansa.
An sace manoman biyu ne yayin da suke hanyar dawowa daga gonarsu da ke Ede/Ileoogbo road a karamar hukumar Ayedire na jihar Osun a ranar Laraba da ta gabata, kuma masu garkuwan suka nemi a biya naira miliyan 25.
Daga bisani masu garkuwan sun yarda sun karbi naira miliyan 6 sannan aka kai musu a wani gari da ke kan iyakar jihar Kogi da Kwara.
Rahotanni sun ce wani majiya na kusa da iyalan, a ranar Laraba ya tabbatar da cewa Samuel da Tobiloba da aka fara sacewa da farko sun shaki iskar yanci.
Hakazalika, wani danginsu da shima yana daga cikin wadanda suka tafi kai kudin fansar shima a sake shi a jihar Kogi. Da aka tuntube shi kan sakinsu, mai magana da yawun yan sandan jihar Osun, Yemisi Opalola ya tabbatar da afkuwar lamarin.










































