Hukumar Yaki da Masu Yiwa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC), ta ce shugabanta, Abdulrasheed Bawa yanzu haka yana cikin koshin lafiya bayan ya samu kulawar likitoci.
A wata gajeriyar sanarwa a ranar Alhamis, mai magana da yawun EFCC, Wilson Uwujaren, ya ce ya fayyace batun ne bayan lamarin da ya faru a Fadar Shugaban Kasa, Abuja a lokacin da yake jawabi a wajen taron bikin Ranar Shaidar dan Kasa, kuma ya kamu da rashin lafiya har ya koma kan kujerarsa.
“Tuni ya sami kulawar likita kuma ya dawo daidai,” in ji Uwujaren.
Karanta Wannan: Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kaduna Ta Kashe Wani Ƙasurgumin Ɗan Bindiga
Tun da farko Solacebase ta ba da rahoton cewa shugaban hukumar ta EFCC ya fadi kasa a wani taron jama’a da aka gudanar a fadar Aso Rock Villa ranar Alhamis.
Idan za a iya tunawa an nada Bawa a matsayin shugaban hukumar EFCC a watan Fabrairu, 2021, a matsayin ma’aikacin hukumar na farko sannan kuma mafi karancin shekaru da ya shugabanci EFCC tun lokacin da aka kirkiro ta.











































[…] Karanta Wannan:Abdurrasheed Bawa Ya Murmure- EFCC […]