Majalisar wakilai, ta bukaci ministar harkokin jin kai da kula da bala’o’i Hajiya Sadiya Farouk da ta yi murabus daga mukamin minista idan har ba ta shirya yin wannan aiki ba.
Hakan ya biyo bayan gazawarta na zuwa gaban kwamitoci daban-daban na majalisar domin kare kudirin kasafin kudin 2023 na ma’aikatar.
Shugaban Kwamitin Kasafin Kudi na Majalisar Wakilai Muktar Betara ya bayyana haka ne a yayin wani zaman bincike kan zargin shigar da kasafin kudin ma’aikatar har na Naira biliyan 206 a cikin kasafin kudin shekarar 2023 a Abuja.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya ya rawaito cewa, an saka samada Naira biliyan 206 da sunan aikin Safety Nets wanda ta ce batasan dalilin cushen ba.
Anasa bangaren shugaban kwamitin da ya fusata ya tambayi dalilin da ya sa Ministar ba ta hallara ba don kare kasafin, ya kara da cewa idan ba ta shirya yin aikin ba to ta yi murabus.
Da take bayyana kura-kuran da aka samu a kasafin kudin ma’aikatar, ministar kudi, Hajiya Zainab Ahmed ta ce ofishin kasafin kudin ne aka yi masa ba daidai ba.
Ta kara da cewa, kamata ya yi ministar harkokin jin kai da kula da bala’o’i ta jawo hankalin ofishin kasafin kudi kan abubuwan da suke ganin dace ba kamar yadda ya faru a sauran ma’aikatu.
Ta ce ma’aikatar tsaro, ma’aikatar wutar lantarki ta tarayya da sauran su ma sun tafka irin wannan kuskure.













































