Hisbah ta kama mutane 31 kan zargin karuwanci da shan barasa

FB IMG 16655913935084210
FB IMG 16655913935084210

Dakarun Hukumar Hisbah a jihar Jigawa sun kama mutane 31 da su ka haɗa da mata 25 a Ƙaramar Hukumar Kazaure da ke jihar a yau Laraba, bisa zargin su da laifin aikata munanan dabi’u.

Kwamandan Hisbah a jihar, Ibrahim Dahiru, ya ce an kama wadanda ake zargin ne da misalin karfe 6 na safe bisa zargin karuwanci da shan barasa.

Ya shaida wa manema labarai a Dutse a yau Laraba cewa, an kama wadanda ake zargin ne a wani samame da hukumar Hisbah ta kai mai taken: “Abin da ka shuka shi za ka girba”.

Kwamandan ya ce an kama kwalabe 55 na barasa iri-iri da kuma lita 50 na Burukutu’ a yayin farmakin.

Ya ce an mika wadanda ake zargin da kayayyakin da aka kama ga ‘yan sanda a yankin domin ci gaba da daukar mataki.

Mista Dahiru ya yabawa mazauna jihar bisa goyon bayan da suke baiwa hukumar Hisbah wajen gudanar da ayyukanta.

Ya kuma bayar da tabbacin cewa Hisbah za ta ci gaba da yaki da munanan dabi’u a duk sassan jihar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here