Wani Kirista mai hidimar Kasa Jeremiah Shimasa Raba, da ke aikin hidimar Kasa a Gusau babban birnin jihar Zamfara ya gina wurin alwala tare da gyara bandaki a wani masallaci.
Ya kuma sanya akwatin bayar da shawarwari a babbar kofar shiga gidan rediyo da talabijin na jihar Zamfara.
Matashin mai shekaru 25 da ke aiki a gidan Rediyo da Talabijin na Jihar Zamfara, ya ce manufar aikin ita ce inganta hadin kai a tsakanin ‘yan Najeriya.
Shimasaan ya ci gaba da cewa, ya dauki matakin ne saboda son da yake yi yaga ana yin alwala musamman ga al’ummar Musulmi a lokacin sallah.
Akwatin shawarwarin a cewarsa shi ne don tattara shawarwari daga al’umma da nufin gudanar da ayyuka.
“Shawarar da na yanke na samar na gudanar da aikin a masallaci shi ne na karfafa hadin kan addini don samar da zaman lafiya a tsakanin mabiya addinai daban-daban.
“Idan dukkanmu a kasar nan za mu mutunta imanin juna, kuma za mu so juna ba tare da wani sharadi ba, za mu samar da ci gaba mai dorewa” in ji shi.

Da yake kaddamar da ayyukan, babban sakataren ma’aikatar muhalli ta jihar Zamfara, Ahmad Liman, ya yabawa Matashin tare da bayyana shi a matsayin mai yunkurin hada kan al’ummar Kasa.
Barista Liman ya ce matasan masu hidimar Kasa irin su Jerry Shimasaan Wanda ke da zuciyar zinare ba kasafai ake samun irin su ba, amma jihar Zamfara ta yi sa’ar samun sa.
Ya ce yanke shawarar daukaka darajar masallacin da wurin alwala babu shakka zai jawo wa matashin albarkar Allah da shiriya da kariyarsa a kowane lokaci.
Babban sakataren ya kuma bukaci sauran matasan da ke kasar nan Kan su yi koyi da irin abin da Shimasaan ya yi wanda a cewarsa zai taimaka matuka wajen samar da zaman lafiya da hadin kai a tsakanin jama’a ba tare da la’akari da duk wani banbanci ba.
Jeremiah Shimasaan ya karanta Turanci da adabi a Jami’ar Jihar Benue da ke Makurdi.
Shi dan hidimar kasa ne na rukunin C kashi na 1 mai lamba ZM/21C/0446 kuma ana sa ran zai kammala shekarar hidimarsa a watan Satumba na wannan shekara.
Wadanda suka halarci kaddamar da ayyukan sun hada da jami’an hukumar kula da masu yi wa kasa hidima (wato NYSC) da sauran masu yiwa kasa hidima da malaman addini da kuma wakilan al’ummar da suka karbi bakuncinsu da dai sauransu.









































