Majalisar Dattawa ta sake sauya dokokinta na tsarin gudanarwa, wani mataki na hana sabbin sanatocin da za su shigo Majalisa ta 11 damar tsayawa takar mukaman shugabanci da na manyan mukamai.
Matakin ya biyo bayan gabatar da wani kuduri da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Lola Ashiru (APC-Kwara), ya gabatar a zaman majalisa na ranar Talata, bayan zaman sirri da ya dauki kusan sa’o’i uku.
Doka ta 4 da ta 5 ne aka sauya a cikin sabon tsarin.
Doka ta 4 ta sauya ta ce: “Zaben sanatoci don zama shugabanni zai kasance bisa tsarin matsayi na sanatoci kuma za a bi shi da tsauri.
Tsarin matsayi shi ne: (i) Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, (ii) Tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, (iii) Tsoffin Manyan Jami’an Majalisar Dattawa, (iv) Sanatocin da suka yi akalla wa’adi ɗldaya na shekaru hudu.
(v) Sanatocin da suka kasance mambobin Majalisar Wakilai (vi). Idan babu i zuwa v, sai sabbin sanatocin da aka zaɓa a karon farko.”
Baya ga tsarin matsayi da aka yi amfani da shi wajen rage damar sabbin sanatocin da za su tsaya takar mukaman shugabanci, Majalisar Dattawa ta kuma saka wani sabon tanadi a Doka ta 5 don hana sabbin ‘yan majalisa tsayawa takar manyan mukamai a Majalisa ta 11 mai zuwa.
Dokar ta ce: “Ba za a ba sanata damar tsayawa takar kowane babban mukami na Majalisar Dattawa ba sai idan ya yi akalla wa’adi biyu a jere kafin a nada shi.”
Wannan na nufin sanatocin da ba su kasance a Majalisa ta 9 da ta 10 ta yanzu ba za su cancanci tsayawa takar mukaman shugabanci a Majalisa ta 11 ba.
Jami’an shugabanci a Majalisar Dattawa su ne Shugaban Majalisa da Mataimakinsa, yayin da manyan jami’ai su ne Shugaban Majalisa, Mataimakin Shugaban Majalisa, Bulaliya da Mataimakin Bulaliya.
Sauran su ne shugabannin jam’iyyu marasa rinjaye da mataimaka jam’iyyu, bulaliya, da mataimakin bulalan jam’iyyu Mara’s a rinjaye. (NAN)










































