Yan daba sun kai hari kan ‘yan kasuwar waya ta farm center, sun jikkata mutane da dama, sun kwashe dukiyoyi a Kano

WhatsApp Image 2026 04 27 at 16.24.54 750x430

An samu tashin hankali a shahararriyar kasuwar waya ta Kano, Farm Centre, bayan da wasu ‘yan daba kusan 200 da ake zargi sun shiga kasuwar, inda suka kai hari kan ‘yan kasuwa tare da sace dukiya.

‘Yan dabar, wadanda aka ruwaito suna ɗauke da adduna da wasu makamai masu hadari, ana zargin sun raka wani mai neman takarar sanatan Kano ta Tsakiya, Abdussalam Abdulkarim, wanda aka fi sani da AA Zaura, zuwa wani taro a wani otal da ke kusa da kasuwar.

Shugaban kasuwar, Alhaji Jamilu Bala Gama, ya tabbatar wa SolaceBase faruwar lamarin a ranar Litinin, yana mai cewa Lamar in ya faru da misalin ƙarfe 1:25 na rana lokacin da ‘yan ta’addan suka mamaye kasuwar.

Ya ce maharan ba Farm Centre kadai suka kai hari ba, har ma sun tayar da hargitsi a wasu kasuwanni uku da ke kusa, ciki har da City Centre da New Dubai.

SolaceBase ta ruwaito cewa al’adar ‘yan siyasa na tafiya tare da ‘yan daba masu dauke da makamai ta zama wani yanayi mai tayar da hankali, wanda sau da yawa ke haifar da tashin hankali da kawo cikas ga harkokin kasuwanci a Kano.

“Suna da yawa, kusan 200 ko ma fiye da haka. Sun kai hari kan mutane da ‘yan kasuwa marasa laifi, suka jikkata su kuma suka sace musu dukiya,” in ji Gama.

A cewarsa, har zuwa lokacin hada wannan rahoto, ‘yan dabar na nan a kewayen wurin da ake gudanar da taron, lamarin da ya tilasta wa ‘yan kasuwa tserewa don neman tsira tare da rufe shagunansu.

Ya kuma bayyana cewa irin wadannan al’amarin ba sabon abu ba ne, yana zargin cewa ‘yan daba sukan bi tarukan siyasa a yankin kuma su kai hari kan ‘yan kasuwa.

“Muna shirin ɗaukar matakin shari’a kan ‘yan siyasar da ke haifar da tashin hankali a kasuwanninmu ta hanyar zagayawa da ‘yan daba,” ya ƙara da cewa.

Gama ya kuma bayyana cewa jami’an ‘yan sanda daga wani ofishi da ke kusa sun kai dauki a yayin faruwar lamarin, amma ‘yan dabar sun kai musu hari, inda aka ruwaito wasu jami’an sun ji rauni.

Wani dan kasuwa, Abdullahi Dabinai, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana shi a matsayin wani ɓangare na wani yanayi da ke faruwa akai-akai wanda ya daɗe yana damun ‘yan kasuwa a yankin.

Ya ce ‘yan sanda sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye don tarwatsa ‘yan dabar, yana mai cewa irin wannan tashin hankali yakan faru a duk lokacin da aka yi wani taron siyasa a kusa.

A cewarsa, duk da cewa harin ya fi mayar da hankali ne a kan shaguna da rumfuna da ke kusa da gefen titi, ‘yan kasuwa da dama na fargabar cewa al’amuran gaba na iya yaɗuwa har cikin kasuwar.

“Akwailokuta da dama da tarukan siyasa suka haifar da tashin hankali, lamarin da ya tilasta wa ‘yan kasuwa kulle kansu a cikin shagunansu don tsira.” Inji shi.

Kawo yanzu, babu wata sanarwa a hukumance daga ‘yan sanda, kokarin jin ta bakin mai magana da yawun Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, bai yi nasara ba, domin bai amsa kiran waya ba.

Kokarin jin ta bakin AA Zaura ma ya ci tura, domin taron da ake alakanta lamarin da shi na ci gaba da gudana.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here