Hukumar shirya jarrabawar shiga jami’o’i da manyan makarantun gaba da sakandire (JAMB), ta yi karin haske kan karuwar cecekuce game da daliban da ke samun sakon ba a saki sakamako ba (No Result Yet), inda ta bayyana cewa an rike sakamakon daliban da ba su kai shekaru ba bisa ka’idojin hukumar.
Mai magana da yawun hukumar, Fabian Benjamin, ya bayyana cewa lamarin ya biyo bayan yawaitar tambayoyi da damuwar da iyaye suka nuna, yana mai cewa daliban da ba su kai shekarun da aka amince da su ba, ba za a fitar da sakamakonsu ba a yanzu, shi ya sa tsarin ke ba da wannan amsa.
Ya jaddada cewa daliban da za su cika shekaru 16 zuwa 30 ga Satumban shekarar 2026 ne kadai za su cancanci zama don rubuta jarrabawar UTME, yana mai jaddada cewa duk wani sabani zai fada karkashin tsarin dalibai na musamman da hukumar ta tanadar.
A karkashin wannan tanadi, dole ne daliban da ba su kai shekaru ba su nuna kwarin gwiwa na musamman a karatu ta hanyar samun akalla maki 320 a UTME kuma su samu akalla kashi 80 cikin 100 a matakan tantancewa na gaba domin a yi la’akari da su don samun gurbin shiga jami’a.
Benjamin ya kara da cewa, bisa yarjejeniyar da aka yi a baya da iyaye, daliban da suka kai maki 320 ne kawai za a zaba kuma a gayyace su don karin tantancewa, lamarin da ya takaita hanyar samun kulawa ta musamman.
Ya tabbatar da cewa har sai an kammala wannan tsari, sakamakon daliban da ba su kai shekaru ba zai ci gaba da kasancewa a rike, ya yi kuma kira ga masu ruwa da tsaki da su yi hakuri yayin da hukumar ke aiwatar da ka’idoji da nufin kiyaye mutuncin tsarin shiga manyan makarantu na kasa.











































