Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya aza harsashin gina babbar makarantar sakandare a yankin Kaura Goje da ke karamar hukumar Nasarawa.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Mustapha Muhammad, ya fitar a ranar Lahadi, an bayyana cewa makarantar idan aka kammala za ta maye gurbin makarantar Maikwatashi wadda ta lalace tare da fuskantar mamayewa, inda aka sayar da wasu sassan filinta ba bisa ka’ida ba.
Abba Kabir Yusuf ya ce ya mika mallakar makarantar Maikwatashi ga Kwalejojin Fasaha da Ilimin Addinin Musulunci ta Jihar Kano domin amfani da ita wajen harkokin ilimi.
Gwamna Abba ya bayyana cewa gina wannan makaranta zai rage wahalar da dalibai ke sha, wadanda a yanzu suke tafiya har Sabon Gari domin zuwa makaranta.
Ya ce akwai dalibai da dama a yankin da suke zuwa Sabongari domin karatu, wanda hakan ya sa gwamnati ta yanke shawarar gina makaranta a wurin.
Gwamnan ya bukaci mazauna yankin da su ba da hadin kai ga dan kwangila, tare da gargadin a yi aikin cikin inganci.
A nasa jawabin, kwamishinan ilimi, Gwani Ali Haruna Makoda, ya ce aikin makarantar zai ci Naira Biliyan 1.3.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa makarantar za ta kunshi ajujuwa 32, dakunan bayan gida 36, da dakunan karatu 4, tare da sauran gine-gine.












































