Tsohon dan wasan gaban kungiyar kwallon kafa ta kasa, Super Eagles, Michael Eneramo ya rasu bayan ya fadi ana tsaka da wasa a jihar Kaduna.
Hukumar kwallon kafa ta kasa (NFF) a ranar Juma’a, ta tabbatar da rasuwar tsohon tauraron dan wasan.
Dan wasan, mai shakara 40 ya yanke jiki ne mintina kadan da dawowa daga hutun rabin lokaci, yayin buga wani wasan sada zumunci a Unguwan Yelwa ta jihar Kaduna
Eneramo ya fara bugawa Najeriya kwallo a wani wasan sada zumunci da tsakanin ta da kasar Jamaica a birnin London na kasar Ingila a ranar 11 ga watan Fabrairun shekarar 2009, wanda aka tashi canjaras.
Ya ci kwallonsa ta farko wa Najeriya a karawar da aka tashi daya da daya tsakanin ta da Jamhuriyar Ireland a birnin London na kasar Ingila a ranar 29 ga watan Mayun 2009
Eneramo scored one of the most important goals that sealed the 2010 World Cup qualification for Nigeria. He scored a late goal as the Eagles eked out a 2-2 draw at home against Tunisia.
Haka zalika, Eneramo ya ci wa Super Eagles kwallo mai matukar muhimmanci a mintin karshe, wanda ya baiwa kungiyar samun tikitin shiga kasar cin kofin duniya, a karawa tsakanin ta da Tunisiya a gida.
Ya buga mintina 10 kacal kafin ya bar taka wa kungiyar ta Super Eagles leda a shekarar 2011
An dai haifi Eneramo a shekarar 1985 a jihar Kaduna, ya kuma fara buga babban mataki a gasar ajin kwararru ta Najeriya a kungiyar kwallon kafa ta Lobi Stars ta garin Makurdi, daga baya kuma ya buga wasa a kungiyoyi a kasashen Tunisiya da Turkiyya kafin ya jingine taka leda a shekarar 2018.













































