Wani sakataren ƙaramar hukuma a Kibiya a jihar Kano ya fada hannun ‘yan bindiga bayan da suka kai hari gidansa da sanyin safiyar ranar Juma’a.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa harin ya faru ne a garin Dinya da misalin ƙarfe 1:00 na dare, kamar yadda shugaban kansiloli na yankin, Hon. Sabo Yusuf Usman, ya bayyana yayin wata tattaunawa da BBC.
Usman ya ce maharan sun samu shiga gidan ne ta hanyar dabara, inda suka yi amfani da ɗan sakataren domin ya kira mahaifinsa.
Yaron, wanda ke kwance a harabar gidan, an tashe shi daga barci sannan aka tilasta masa ya kira mahaifinsa.
Da suka yi kiran, yaron ya sanar da mahaifinsa cewa yana fama da ciwon ciki, domin ya sa shi bude ƙofa.
Da yake yana tunanin ɗansa na cikin matsala, sakataren ya bude ƙofar gidan, amma sai ya gamu da ‘yan bindigar da ke dauke da makamai.
Daga nan ne suka tafi da shi tare da ɗansa, amma daga baya suka saki yaron, suka tafi da sakataren kafin jami’an tsaro su kai dauki.
Ko da yake yankin Kibiya ya kasance cikin kwanciyar hankali a baya, ƙananan hukumomi makwabta kamar Tsanyawa da Shanono, waɗanda ke makwabtaka da jihar Katsina, sun fuskanci hare-haren ‘yan bindiga a baya-bayan nan.













































