Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, a matsayin shugaban Kwamitin Ciyar da Jama’a na ƙasa a watan Ramadan.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun sarkin, Abubakar Balarabe Kofar Naisa, ya fitar a ranar Alhamis.
Sanarwar ta ce an sanar da naɗin ne yayin wata ziyara da tawagar gwamnatin tarayya ta kai fadar sarkin da ke Gidan Nassarawa.
Tawagar ta haɗa da Farfesa Muhammad Kabir, Limamin Ƙasa na Babban Masallacin Abuja, da Babban Sakatare Injiniya Muhammad Adamu, da Mataimakin Darakta na Kayayyaki Alhaji Yahaya Abdulhadi, duk daga ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, da Malam Muktar Sarki da Alhaji Alhassan Ibrahim.
Tawagar ta bayyana cewa an zaɓi sarkin ne bisa cancanta da ƙwarewarsa wajen jagoranci.
A cewar sanarwar kwamitin ba na siyasa ba ne, shiri ne na gwamnatin tarayya domin hidimtawa jama’a a watan Ramadan.
Kwamitin zai kula da rabon kayan abinci na masarufi da suka haɗa da shinkafa, gero da man girki ga waɗanda suka cancanta a faɗin ƙasa.
Sanarwar ta ce a shekarun baya shirin ya fi ta’allaka ne kan shirya buɗa-baki da shugaban ƙasa ke yi wa zaɓaɓɓun shugabanni.
Sai dai a wannan karo, shugaban ƙasa ya umarci a faɗaɗa shirin domin ya shafi rabon kayan abinci a shiyyoyi shida na ƙasar nan.
Kwamitin na aiki ne ƙarƙashin jagorancin gwamnatin tarayya tare da haɗin gwiwar mahukuntan Babban Masallacin Ƙasa da ke Abuja da wasu mambobin Majalisar Tarayya, ciki har da Sanata AbdulRahman Kawu Sumaila da Hon. AbdulSamad Sambo Dasuki, da sakatarori uku da daraktoci huɗu.
Haka kuma, shugaban kwamitin amintattun Babban Masallacin Ƙasa, Alhaji Yahaya Abubakar, ya umurci limamai na ƙasa da daraktoci biyu daga masallacin su bayar da cikakken goyon baya ga kwamitin.
Kwamitin na ƙarƙashin kulawar Sakataren Gwamnatin Tarayya.
Tawagar ta nuna ƙwarin gwiwa cewa Sarkin Kano na 15 zai ba da jagoranci mai kyau domin nasarar shirin.
A nasa jawabi, Sarkin ya yaba da matakin faɗaɗa shirin ciyarwar, yana mai cewa lokaci ne mai dacewa a wannan wata mai albarka.
Ya gode wa Allah da ba shi damar yin hidima, tare da fatan za a dore da shirin domin samar da sauƙi ga jama’a na dogon lokaci.
Ya kuma tabbatar da cewa kwamitin zai sauke nauyin da aka ɗora masa yadda ya kamata, tare da ba da shawarwari da goyon bayan da ya dace domin nasarar aikin.













































