Kasar Morocco ta samu gurbin buga wasan ƙarshe na gasar cin kofin Afirka bayan ta doke Najeriya da ci 4–2 a bugun fenariti, bayan wasan daf da na ƙarshe ya kare babu ci ko daya har bayan ƙarin lokaci.
Wasan ya gudana a filin wasa na Prince Moulay Abdellah da ke Rabat, inda dubban magoya baya suka shaida fafatawar mai tsauri.
Mai tsaron ragar Morocco, Yassine Bounou, ya taka muhimmiyar rawa wajen nasarar tawagarsa bayan ya hana Samuel Chukwueze da Bruno Onyemaechi zura kwallo a bugun fenariti.
Wannan ya bai wa Youssef En-Nesyri damar zura bugun fenaritin karshe da ya tabbatar da nasarar Morocco, lamarin da ya haddasa murnar ban mamaki a filin wasan.
A bangaren ‘yan wasan Morocco, Hamza Igamane ya fuskanci yanayi mai wahala bayan mai tsaron ragar Najeriya Stanley Nwabali ya hana shi zura kwallo a bugun fenariti.
Duk da haka, sauran ‘yan wasan Morocco ciki har da kyaftin Achraf Hakimi sun cika nasu bugun fenariti, abin da ya tabbatar da nasarar tawagar baki daya.
Morocco za ta kara da Senegal a wasan ƙarshe da za a buga a ranar Lahadi, bayan Senegal ta doke Masar da ci 1–0 a ɗayan wasan daf da na ƙarshe.
Sadio Mane ne ya zura kwallon da ta ba Senegal nasara a kan Masar din da Mohamed Salah ke jagoranta.
Wasan ƙarshe tsakanin Morocco da Senegal na nuni da haduwar manyan kasashe biyu mafi daraja a nahiyar Afirka bisa jerin FIFA, abin da ke kara wa gasar armashi.
Tawagar Morocco karkashin jagorancin Walid Regragui na fuskantar matsin lamba mai yawa domin kawo wa kasarsu kofin Afirka na farko cikin kusan shekaru hamsin, tare da amincewa da goyon bayan magoya baya a Rabat.
A daya bangaren, wannan sakamako ya kawo karshen burin Najeriya ta hanya mai radadi, shekaru biyu bayan ta sha kashi a wasan ƙarshe a hannun masu masaukin baki a Kasar Ivory Coast.
AFP













































