Sojoji sun ceto wanda aka yi garkuwa da shi, tare da kwato shanun da aka sace a Kano

WhatsApp Image 2025 12 28 at 07.01.34 1 720x430

Sojojin rundunar haɗin gwiwa ta tsaro sun ceto wani mutum da aka sace daga hannun ‘yan bindiga a safiyar Lahadi a jihar Kano, bayan samun bayanan sirri kan motsin ‘yan bindigar da ke shirin kutsawa yankin.

Sojojin da ke aiki a yankin Yankwada sun samu bayanai cewa wasu ‘yan bindiga daga yankunan Daurawa da Kira a jihar Katsina na tunkarar kan iyakar Kano, lamarin da ya sa suka kai farmaki tare da fafatawa da su a wani mummunan artabu.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa a yayin wannan samame, an ceto Rabiu Alhaji Halilu mai shekaru 38, wanda aka sace tun da farko, tare da kuɓutar da shi daga hannun masu garkuwa da mutane.

Rahotanni sun bayyana cewa Halilu ya samu raunin harbin bindiga a ƙafarsa, inda aka gaggauta kai shi cibiyar lafiya ta rundunar haɗin gwiwa a Faruruwa domin samun kulawar likitoci.

A yayin da ‘yan bindigar suka tsere daga filin artabun, sojojin sun kwato babura guda biyu da aka bari a baya, tare da kwato wasu shanu da aka sace, kodayake ba a fayyace adadin shanun ba.

Mai magana da yawun rundunar sojoji ta Brigade ta uku Manjo Babatunde Zubairu ya tabbatar da faruwar lamarin ga jaridar Solacebase, inda ya bayyana cewa sojojin sun fatattaki ‘yan bindigar har zuwa yankin Matazu a ƙaramar hukumar Katsina, kuma sun ci gaba da kasancewa cikin shiri domin tabbatar da tsaron yankin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here