Akalla mutane 54 ne suka mutu sakamakon cizon maciji a jihar Gombe a shekarar 2025, a cewar jami’in kula da yaduwar cututtuka na ma’aikatar lafiya ta jihar Gombe, Dakta Nuhu Bile.
Dakta Bile ya bayyana hakan ne a birnin Gombe yayin taron kwamitin kula da lafiyar jama’a cikin gaggawa na jihar.
Taron wanda asusun tallafawa yara na Majalisar Ɗinkin Duniya UNICEF ya tallafa, kuma mataimakin gwamnan jihar Gombe, Manassah Jatau, ya jagoranta a matsayinsa na shugaban kwamitin.
Ya bayyana cewa a cikin shekarar 2025, an samu jimillar rahotannin cizon maciji 1,591 da aka kai asibitin kula da cizon maciji da ke Kaltungo, inda mutuwar mutane 54 ke wakiltar kashi 3.4 cikin 100 na adadin, yayin da aka kula da sauran marasa lafiya aka sallame su.
A cewarsa, adadin cizon maciji da aka samu a 2025 shi ne mafi ƙanƙanta cikin shekaru huɗu da suka gabata, inda aka samu rahotanni 2,794 a 2022, 2,594 a 2023, da kuma 2,189 a 2024.
Dakta Bile ya ce raguwar adadin ba wai saboda raguwa ne a yawaitar cutar ba, sai dai sakamakon ƙarancin maganin dafin maciji kyauta kuma isasshe a asibitin, lamarin da ya tilasta mutane da dama komawa neman magani ta wasu hanyoyi na daban.
Ya ƙara da cewa yawancin waɗanda cizon maciji ya shafa kan zo asibiti ne kawai idan lamarin ya tsananta, saboda rashin samun maganin dafin maciji kyauta, lamarin da ke ƙara haddasa mutuwar wasu daga cikinsu.
Game da cutar kwalara, ya bayyana cewa an samu mutane 176 da suka kamu da cutar a jihar Gombe a 2025, inda mutane biyar suka mutu, yayin da aka samu rahotannin cutar Lassa guda 14 da mutuwar mutane takwas.
A nasa jawabin, Dakta Jibril Muhammad daga ofishin ƙasa na asusun tallafawa yara na Majalisar Ɗinkin Duniya UNICEF a Abuja ya ce taron na daga cikin ƙoƙarin asusun na inganta lafiyar jama’a a jihohi, tare da bayyana cewa taron ya haɗa jami’an lafiya daga jihohin Gombe, Bauchi, Adamawa da Plateau.
Ta jaddada muhimmancin aiwatar da tsare-tsaren da aka tsara domin shawo kan barkewar cututtuka.
NAN













































