DA DUMI-DUMI: Majalisar wakilai zata sake duba kudirin dokokin mata da aka gaza aiwatarwa 

Reps
Reps

Majalisar wakilai ta kuduri aniyar sake duba kudurorin da ba su yi nasara ba domin inganta muradun mata a gyaran kundin tsarin mulkin da ake yi.

A ranar Talata, kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila ya ce za a yi hakan nan da wasu makonni masu zuwa.

Hakan dai ya zo ne a daidai lokacin da dubban mata suka sake tare babbar kofar shiga majalisar dokokin kasar domin nuna adawa da abin da suka bayyana a matsayin rashin adalcin da ake yi wa mata a kasar.

Matan da suka yi zanga-zangar da suka tare kofar Sakatariyar Tarayya ta Majalisar, sun yi zanga-zangar kin amincewa da kudirin dokar jinsi yayin da aka yi wa kundin tsarin mulkin kwaskwarima a makon jiya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here