Kafa sabuwar hukumar Hisba mai zaman kanta da Ganduje ke niyya ba ta dace da kundin tsarin mulki ba, kuma barazana ce ga zaman lafiyar jiha – Lauya

Abdullahi Umar Ganduje 1

Lauya mai fafutukar kare haƙƙin ɗan Adam kuma mai sharɓi kan harkokin kundin tsarin mulki Hamza N. Dantani, ya bayyana cewa, shirin tsohon gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, na kafa wata hukumtar Hisbah mai zaman kanta domin tsoffin ma’aikatan Hisbah 12,000 da aka sallama, ya saba wa kundin tsarin mulkin Najeriya kuma barazana ce ga ikon gwamnati mai ci.

Dantani ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya sanya hannu cewa wannan yunkuri kuskure ne a tsarin mulki domin ya yi kama da neman karɓe ikon da kundin tsarin mulki na 1999 ya tanadar wa gwamnati mai ci kadai.

Ya ce abin mamaki ne yadda tsohon gwamna zai nemi kafa wata sabuwar hukuma mai kama da tilastawa doka ba bisa tsarin mulkin jihar ba.

Ya jaddada cewa kundin tsarin mulki ya fayyace a sashe na 176(2) cewa gwamna shi ne babban jami’in gudanarwa na jiha, don haka Ganduje da ba shi ne gwamna ba, ba shi da ikon aiwatar da duk wata tafiyar da ta shafi ayyukan gwamnati ko tsaro.

Lauyan ya yi nuni da cewa Kano na da hukumar Hisbah ta doka wadda ke ƙarƙashin ikon gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, kuma duk wani gyara ko shiri ya kamata a miƙa shi ga gwamna ko majalisar dokokin jihar.

Ya ce duk wani yunƙuri da ya kai ga kafa sabuwar hukuma ba bisa doka ba zai haifar da rikice-rikice a tsari da tsaro.

Karanta: Gwamnan Kano ya baiwa rundunar tsaro ta JTF tallafin Motoci da Babura

Dantani ya yi gargadin cewa kafa sabuwar Hisbah mai zaman kanta na iya zama barazana ga harkokin tsaro, domin harkokin ’yan sanda da tsaro na cikin jerin ayyukan da tsarin mulki ya bai wa gwamnatin tarayya kaɗai.

Ya bayyana cewa kamar yadda doka ta tanada, jihohi za su iya kafa hukumomin addini ko al’ada kamar Hisbah, amma dole su kasance ƙarƙashin ikon gwamnati ba na mutum ɗaya ba.

Ya kara da cewa duk wani yunƙurin tattara tsoffin ma’aikatan Hisbah domin kafa sabuwar hukuma mai zaman kanta zai yi kama da kafa rundunar rikici, wanda kundin tsarin mulki ya haramta a sashe na 227.

Dantani ya bayyana wannan shiri a matsayin ɗaukar matakin siyasa da kuma kalubalantar gwamnatin Abba Kabir Yusuf kai tsaye.

Dan rani ya shawarci Ganduje da ya janye wannan tunani da ya kira da haɗari, ba bisa doka ba, yana mai cewa hikima da mutunta tsarin mulki ya kamata su yi tasiri a wannan lamari domin kare zaman lafiya da doka a Jihar Kano.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here