APC ta kai ƙorafin Minista Ata ga shugaban kasa Tinubu kan zarge-zargen yin magana ba bisa ƙa’ida ba

Housing Minister. Yusuf Abdullahi Atta 750x430

Jam’iyyar APC a Kano ta aikawa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu wasiƙar ƙorafi kan Alhaji Yusuf Abdullahi Ata, minista a ma’aikatar gidaje da cigaban birane, bisa kalaman da ya yi cikin ’yan kwanakin nan game da harkokin cikin jam’iyya da ’yan takara.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa jam’iyyar ta bayyana damuwa cewa irin waɗannan kalamai na iya jawo rashin fahimta da rarrabuwar kai tsakanin ’ya’yan jam’iyyar.

A cikin wasiƙar da aka rubuta a ranar 21 ga Nuwamba 2025, wadda shugaban APC na Kano, Alhaji Abdullahi Abbas ya sanya wa hannu, jam’iyyar ta jaddada cewa batutuwan da suka shafi harkokin cikin gida na jam’iyya “na karkashin ikon shugabancin APC da masu magana da yawunta kadai”.

Ata ya soki yadda aka sake nada shugaban APC na Kano, Abdullahi Abbas, yana mai cewa hakan na iya raunana damar jam’iyyar a gaba.

Karanta: Takarar Gwamna 2027: Ƴan Majalisa daga Kano sun goyi bayan Sanata Barau ya yi takarar Gwamna domin shi yafi dacewa

Ya kuma yi bayanin cewa zai iya barin jam’iyyar idan aka cigaba da rike kujerar, amma daga bisani ya ce an karkatar da kalamansa kuma sun fito ne domin ƙarfafa haɗin kan jam’iyya, ba akasin haka ba.

Wasiƙar ta kuma ja hankalin cewa a matsayinsa na minista, kalamansa na jama’a na iya fassaruwa a matsayin matsayar jam’iyya, wanda hakan zai iya janyo rikice-rikice.

Haka kuma ta bayyana cewa duk da ’yancinsa na goyon bayan duk wani ɗan takara, matsayinsa a majalisar zartarwa ta tarayya na bukatar ya rika furta kalamai da ke haifar da haɗin kai, ba sabanin haka ba.

APC ta gargadi Ata cewa cigaba da irin waɗannan kalamai na iya kaiwa ga ɗaukar matakin ladabtarwa.

Tuni an aika kwafen wasiƙar ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, shugaban APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Goshwe Yilwatda, tsohon gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje, da mataimakin shugaban APC na Arewa maso Yamma.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here