Rundunar ’yan sanda ta fara bincike kan zargin karɓar rashawa na Dala Miliyan 10 da Alwan Hassan ya yi wa shugaban majalisar dattawa Godswill Obot Akpabio da mataimakinsa Barau I. Jibrin, game da dakatar da tabbatar da Abdullahi Garba Ramat a matsayin shugaban Hukumar Kula da Lantarki ta Najeriya.
Alwan ya bayyana a wata hira da aka yi da shi a Kano cewa manyan masu ruwa da tsaki a fannin wutar lantarki ne suka bayar da kuɗin domin hana tantance Ramat.
Rundunar ’yan sanda ta gayyaci Alwan domin ya tabbatar da zarge-zargen da ya yi kan waɗannan manyan jami’an majalisar dattawa.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa an kama Alwan a sashen binciken manyan laifuka da ke Abuja bayan da ya amsa takardar gayyata daga ’yan sanda.
Mwata majiya ta bayyana cewa ana buƙatar Alwan ya fayyace sunayen mutanen da ya ke cewa su ne suka bayar da kuɗin, lokacin bayarwar da kuma yadda aka gudanar da al’amarin.
Rundunar ta ce tana buƙatar cikakkun bayanai kan waɗannan zarge-zarge domin ci gaba da bincike.
Tun a makon da ya gabata, majalisar dattawa ta musanta zargin cewa shugabanninta sun karɓi kuɗi domin hana tantance Ramat.
Kakakin majalisar, Sanata Yemi Adaramodu, ya bayyana ikirarin a matsayin abin da ba shi da tushe tare da bayyana shi a matsayin ƙoƙari na ɓata suna.
Majalisar ta bayyana cewa dakatar da tantancewar Ramat ya biyo bayan korafe-korafen jama’a da dama da suka shafi sunansa, wanda a bisa tsarin majalisar ya sanya dole a dakata da nazarin sunan kowane ɗan takara da ke fuskantar muhawarori ko koke-koke masu nauyi, wanda hakan ya taba faruwa da wasu ’yan takara a baya.
Majalisar Dattawa ta nanata cewa ba za ta yarda a matsa mata lamba ta hanyar zarge-zargen da ba su da tabbaci ba, sannan ba za ta bari wani ya rage kimarta ba.
Ta kuma ce, za ta gurfanar da Alwan a gaban kotu domin ya gabatar da hujjojin da zai tabbatar da zarge-zargen da ya yi.
A halin da ake ciki, rundunar ’yan sanda ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da gudanar da bincike kan wannan batu domin gano gaskiyar lamarin, tare da tabbatar da cewa duk masu ruwa da tsaki za su bayyana gaskiya a gaban hukuma.












































