Shugaban kwamitin riko na jam’iyyar APC Mai Mala Buni ya bayyana ranar 26 ga watan Fabrairu a matsayin ranar gudanar da babban taron jam’iyyar APC.
Mai Mala Buni, wanda kuma shi ne gwamnan jihar Yobe, ya bayyana hakan ne a ranar Talata a wurin taron matan jam’iyyar APC na kasa na shekarar 2022, wanda aka gudanar a babban dakin taro na kasa ICC da ke Abuja.
Ya ce jam’iyyar tana neman goyon bayan matan jam’iyyar don gudanar da babban taron cikin nasara.
Cikakkun bayanai daga baya.













































