Rundunar jami’an hadin gwiwa ta Operation Hadarin Daji ta Arewa maso Yamma sun kama wani fitaccen shugaban ‘yan bindiga, Usman Abubakar, wanda aka fi sani da Harinde a jihar Zamfara.
Harinde, mai shekaru 35 shugaban ‘yan fashin an kama shi ne ranar Alhamis a Shinkafi bayan wani rahoton sirri da aka samu.
Ya fito daga kauyen Kukatara da ke karamar hukumar Shinkafi ta jihar kuma shi ne shugaban sansanin ‘yan bindiga da ke kauyen, kwamandan wani fitaccen jarumin ‘yan fashi da makami a kasashen yammacin Afirka Kachalla Halilu Sububu.
Wanda ake zargin Usman Harinde yana da alhakin daruruwan hare-hare, garkuwa da mutane, satar shanu, da sauran miyagun ayyuka a kewayen Shinkafi, Boko-Faru-Janbako a karamar hukumar Zurmi, da sauran kauyukan jihar Sokoto, a cewar rundunar.
Daga cikin abubuwan da aka karbo daga hannun sa akwai kudi, laya, da kakin soja.
A baya-bayan nan ne sojojin suka kama wani kasurgumin sarkin da ke addabar Tsafe West a karamar hukumar Tsafe wanda kuma ya amsa laifin kashe wasu jami’an ‘yan sanda guda biyu a yankin.













































