A ranar Larabar da ta gabata ne hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC ta gurfanar da Olu Agunloye, tsohon ministan wutar lantarki a gaban kotu bisa zarginsa da laifin zamba cikin aminci.
Karanta wannan: AFCON: Ta bawa NTA damar yada gasar wasanni 52
An gurfanar da Agunloye a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja inda ya ki amsa laifin da ake tuhumarsa.
Karanta wannan: Gwamnatin Najeriya ta wofintar da mu a Sudan-Wasu Dalibai
Alkalin kotun, Mai shari’a Donatus Okorowu ya bayar da umarnin a cigaba da tsare tsohon ministan a gidan gyaran hali na Kuje har sai an saurari bukatar neman belinsa.













































