Tsaro: Buhari ya tura shugabannin tsaro zuwa Sokoto da Katsina

5155E1C5 F749 4498 90A2 0FB2906E5E05
5155E1C5 F749 4498 90A2 0FB2906E5E05

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aika da tawaga ta musamman zuwa jihohin Sokoto da Katsina wanda suke fama da matsalar rashin tsaro.

Wannan na zuwa ne dai-dai lokacin da yan  bindiga ke ci gaba da kai hare-hare a yankunan jihohin, wanda ta sanya aka fara zanga-zanga a wasu jihohin arewa.

Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa Malam Garba Shehu ya fitar tace shugaban kasa Buhari  yana jiran rahoto cikin gaggawa da kuma shawarwari kan matakin da ya kamata a dauka domin magance matsalolin da jihohin ke fuskanta.

Cikin waɗanda Buharin ya tura akwai babban mai ba shi shawara kan harkokin tsaro Manjo Janar Babagana Monguno mai ritaya da Babban Sufeton ƴan sandan Najeriya Usman Alkali Baba da daraktan hukumar tsaro ta farin kaya Yusuf Magaji Bichi da daraktan hukumar tattara bayanan sirri ta Najeriya Ahmed Rufa’i Abubakar da kuma shugaban tsaro na rundunar sojin Najeriya Manjo Janar Samuel Adebayo.

Sanarwar ta kara jaddada kudirin gwamnatin tarayya na ganin an kawo karshen ‘yan bindiga da sauran ‘yan ta’adda wanda ke barazana ga rayuwar al’ummar kasar nan.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here