Zanga-Zanga Kan Rusau Da Gwamnatin Abba Gida Gida Ke Yi

Protesters in Kano
Protesters in Kano

Masu zanga-zanga sun cika titunan birnin Kano don nuna damuwarsu kan rushe-rushen da gwamnatin jihar ta Abba Gida Gida ke yi. Daily Trust ta tattaro cewa gwamnatin Kano ta rusa gine-gine da dama a jihar yayin da take shirin ci gaba da rushe-rushen da ke jawo asarar dukiyoyi.

Gwamnatin ta sha fada cewa za ta ci gaba da rusau din akan shaguna ko gidajen da aka gina ko mallaka ba bisa ka’ida ba.

Daga cikin gine-ginen da gwamnatin ta rushe akwai tsohon otal din Daula da manyan kantuna a filin Polo da kuma filin Idi.

Yayin da gwamnatin ta saka jan layi don rushe wasu gine-gine a Salanta da ke kan hanyar BUK a birnin Kano. Da yake magana a madadin masu zanga-zangar, Kwamared Zahradeen Sani Bala ya ce ya kamata idan Abba Gida Gida ya na da wani matsala da tsohon ya kira shi ya amsa laifukansa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here