Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama wani da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi mai suna Hafizu Ali mai shekaru 25, tare da wasu mutane biyar da ake zargin ɓata-gari ne, a wani samame da jami’an ’yan sanda na sashen Jaoji suka gudanar a jihar Kano.
Aikin samamen, wanda aka gudanar bisa umarnin kwamishinan ’yan sandan jihar Kano, Ibrahim Bakori, ya haifar da kwato kwayoyin maganin Pregabalin guda 2,070 da ake zargi, fakiti 23 na tabar wiwi da ake zargi, wukake huɗu, almakashi biyu da kuma gatari guda.
Hakan na ƙunshe a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ’yan sandan jihar Kano, CSP Abdullahi Kiyawa, ya fitar a Kano ranar Litinin.
A cikin sanarwar, kwamishinan ’yan sandan, Ibrahim Bakori, ya yaba wa jami’an da suka gudanar da aikin bisa jajircewarsu, tare da gode wa al’ummar jihar bisa goyon bayan da suke bai wa rundunar.
Sanarwar ta kuma nuna cewa bayan kammala bincike, za a gurfanar da waɗanda ake zargi a gaban kotu domin fuskantar hukunci bisa doka.
Rundunar ’yan sandan ta buƙaci jama’a da su ci gaba da bayar da rahoton duk wani abu mai tayar da hankali ko bayanan sirri zuwa ofishin ’yan sanda mafi kusa, ko kuma su tuntubi rundunar ta lambobin wayar da aka ware domin gaggawa.













































