Ƴan kasuwa a Kano na ƙera babura masu lantarki, suna haskaka baiwar Najeriya

WhatsApp Image 2025 09 19 at 20.00.39 750x430

Najeriya ba ta da arzikin albarkatun ƙasa kawai, amma tana da matasa da ƙwararru masu fasaha da baiwa da ke ƙirƙira abubuwa duk da ƙarancin dama.

Ɗaya daga cikin misalai na musamman ita ce Hajiya Rukayya Khalid, wata ‘yar kasuwa daga Kano wadda ta fara ƙera babura masu amfani da lantarki daga kayan cikin gida domin rage kuɗin sufuri da kuma rage gurbata muhalli.

A tattaunawarta da jaridar Solacebase, Hajiya Rukayya, wadda ta kafa kamfanin Prestige Tricycle Nigeria Limited, ta ce sha’awarta na dogaro da kai da ƙirƙira ne ya ja hankalinta zuwa wannan aiki.

Kafin nan, ta yi fice a harkar samar da takin zamani na ruwa, amma bayan kasuwar ta yi sanyi, ta dawo ga burinta na shekaru — ƙera babura masu lantarki.

Ta bayyana cewa shekaru kusan biyar da suka gabata ta gaya wa ’ya’yanta cewa wata rana za ta gina babur mai lantarki kamar wanda ta gani a wata hoto, kuma yau wannan buri ya fara zama gaskiya. Kamfaninta ya riga ya kera samfurori 12 gaba ɗaya, ciki har da sabon salo da ta ce ya bambanta da duk abin da ake gani a titunan Najeriya.

Sabbin baburan da take ƙera suna da injinan zamani masu ɗorewa, sauƙin gyara da kuma rahusa idan aka kwatanta da na al’ada. Duk da ba ta je jami’a ba, Rukayya ta ce Allah ne ya ba ta basira da ƙarfin zuciya da ta sa ta cimma wannan nasara.

Labarinta na nuna irin hazaka da baiwa da ke cikin matasan Najeriya, waɗanda da tallafi mai kyau za su iya ƙirƙirar mafita da za ta iya gogayya a duniya.

Ta yi kira ga gwamnati da masu ruwa da tsaki su rungumi irin waɗannan ƙirƙira, saboda a wasu ƙasashe ana ba da cikakken goyon baya ga masu ƙirƙira har sai ya amfanar da al’umma baki ɗaya.

Ta kuma yi kira ga matasa da su yi amfani da damar da suke da ita wajen gwada basirarsu ba tare da tsoro ba.

A cewarta, nasarar ƙasarmu ba ta ta’allaka ga albarkatun ƙasa kaɗai ba, amma ga mutane da basirarsu, waɗanda za su iya sauya tattalin arzikin Najeriya ta hanyar mafita na cikin gida.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here