
Rundunar ‘ƴan sanda a Abuja babban birnin Najeriya ta ce ta kama wasu mutane 15 da ake zargi da hannu wajen fasa rumbun adana abinci a birnin.
Wasu matasa ne suka fasa rumbun ajiya kayan abincin na hukumar kai gajin gaggagawa ta ƙasar, a yankin Gwagwa.
Bayanai sun nuna cewa matasa sun yiwa rumbun ƙarƙaf, ko da yake ‘ƴan sandan sun ce sun kwato buhu 26 na masarar da ake zargin an kwashe.
Karin labari: Hatsarin mota ya yi sanadiyar mutuwar mutum 12 da jikkatar mutum 28
‘Ƴan sandan sun kuma ce sun kwato babura 5 daga mutanen da aka cafke.
A ƙarshen mako ne wasu matasa suka dakawa wata babbar mota mai ɗauke da taliya wawa, kuma har yanzu babu rahoton kama wani.
matsalar fasa rumbun abinci ko motocin da ke ɗauke da kayan abinci, batu ne da ke ci gaba da faruwa a sassan ƙasar daban-daban.
Karin labari: Kungiyoyin matasa a jihar Ogun sun bukaci Tinubu ya bude boda
Miliyoyin ‘ƴan ƙasar ne ke rayuwa cikin ƙangin talauci, lamarin da ya jefa da dama cikin halin yunwa da ƙarancin abinci.
Tun bayan janye tallafin mai a watan Mayun da ya gabata ne, farashin kayayyaki, musamman na abinci suka yi tashin gwauron zabi a ƙasar.












































