‘Ƴan kasuwar Nijar sun yi watsi da ƙayyade farashin shinkafa

'yan kasuwa, shinkafa, nijar, watsi, kayyade, farashin
'Ƴan kasuwa a jamhuriyar Nijar sun bijirewa dokar da ministan kasuwacin kasar ya sanyawa hannu da ke ƙayyade farashin shinkafa a fadin kasar...

‘Ƴan kasuwa a jamhuriyar Nijar sun bijirewa dokar da ministan kasuwacin kasar ya sanyawa hannu da ke ƙayyade farashin shinkafa a fadin kasar.

‘Ƴan kasuwar sun ce gwamnatin ta ɗauki matakin ne ba tare da yin shawara da su ba.

Dan haka suka ce yin biyayya ga wannan doka zai haifar musu da asara, ko ma ya janyo musu karyewar jari.

Karin labari: Ƙungiyar malaman Senegal sun yi watsi da yin zabe a watan Yuli

Shugaban ‘ƴan kasuwar Alhaji Sani Shekarau ya ce idan suka yi amfani da farashin gwamnatin za su iya durƙushewa.

Al’ummar ƙasar ne suka fara kokawa kan rashin biyayyar da ‘ƴan kasuwar su ka yi ga dokar.

Karin labari: “Za’a Iya Gudanar Da Zabe Ta Hanyar Amfani Da Na’urorin Zamani A Najeriya” – El-Rufa’i

Ma’aikatar kasuwancin ta ce ta ɗauki matakin ƙayyade farashin shinkafar ne bayan ta yi la’akari da hauhawar farashinta da kuma irin wahalar da mutane ke sha.

Wasu mazauna Yamai babban birnin ƙasar sun ce babu irin shinkafar da aka ƙayyade mata farashin a kasuwanni.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here