Ƙungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars, ta sanya hannu kan wata yarjejeniyar hadin gwiwa da ta kai Naira miliyan 100 da gidan rediyon Faransa RFI Hausa, domin tallafa wa ƙungiyar da kuma tallata kafar yaɗa labaran.
An bayyana hakan ne a yayin wani taron da aka gudanar yau Alhamis a filin wasa na Sani Abacha da ke Kano, wanda ya samu halartar jami’ai daga Kano Pillars da RFI Hausa.
Da yake jawabi a wajen taron, Babban Manajan kungiyar Kano Pillars kuma tsohon kyaftin din Super Eagles, Ahmad Musa, ya bayyana hadin gwiwar a matsayin wani babban ci gaba ga kungiyar da kuma al’ummar Kano.
Ya kuma ƙara da cewa yarjejeniyar za ta ƙara haɓɓaka kafafen yaɗa labarai na kungiyar da kuma taimaka wa wajen yin tambari da aiki.
Ya bayyana cewa tallafin ya haɗa da na’urori na zamani kamar na’urorin daukar hoto da na’ura Kwamfutoci da horar da kafafen yada labarai na wata-wata ga jami’an yaɗa labarai na ƙungiyar da sabuwar riga da RFI ta ɗauki nauyin samar wa.
SolaceBase ta ruwaito cewa an ƙaddamar da samfurin kayan aikin da ke ɗauke da kayan gargajiya na Kano a yayin bikin.
Shi ma da yake magana, shugaban sashen Hausa na Najeriya na kafar, Joseph Pelly, ya ce hadin gwiwar na da nufin taimakawa wajen ɗaukaka martabar Kano Pillars a duniya.
Ya kuma yi nuni da cewa, RFI Hausa za ta kuma tallafa wa harkokin ƙungiyar da kuma faɗaɗa hanyoyin sadarwa na zamani.
Haɗin gwiwar kuma ya shafi dukkan nau’ikan ƙungiyar gami da babbar ƙungiyar da ƙungiyar ta biyu watau Junior Pillars da ƙungiyoyin matasa kamar na ƴan ƙasa da shekaru 13 da 15 da kuma na ƴan ƙasa da shekaru 19 watau U-13, U-15, da U-19.
Ahmad Musa ya bukaci sauran kamfanoni da ƙungiyoyi da daidaikun jama’a da su haɗa hannu da ƙungiyar, inda ya ce ƙungiyar Kano Pillars a shirye ta ke ta ƙara haɗa kai da za ta taimaka wajen bunƙasa ƙungiyar.
Waɗanda suka halarci taron sun haɗa da Janar Manaja na Kano Pillars tsohon kyaftin din Super Eagles, Ahmad Musa da shugaban ƙungiyar Ali Na yara da membobin hukumar.
Wakilin RFI Hausa shi ne shugabanta na Najeriya Joseph Pelly da Babban Editan kafar Bashir Ibrahim Idris da shugaban sashen kafofin sadarwa da na sada zumunta na zamani na RFI Abdulrahman Gambo.












































