Zargin Almundahanar Naira Miliyan 188.6: Hukumar yaki da cin hanci ta Katsina na bincikar kansiloli da malamai kan badakalar taki da kuɗin makaranta

KATSINA map

Hukumar Korafe-korafe da ƴaki da cin hanci ta Jihar Katsina (KTPCACC) ta fara bincike kan zargin almundahana da ya kai naira miliyan 188.6, da ya haɗa da badakalar rabon taki na tallafi daga kansiloli da jami’an raya ƙauyuka, da kuma ɓatar da kuɗin makarantu da na Ma’aikatar Banki da Kudi ta jihar.

A cewar wata sanarwa daga hukumar, binciken farko ya nuna cewa kansiloli da jami’an hukumar raya al’umma sun karkatar da naira 46,061,000 a lokacin rabon taki na tallafi ƙarƙashin shirin raya ƙauyuka.

Wasu daga cikin wadanda ake zargi sun amince da laifin tare da fara mayar da kuɗin, yayin da wasu ake ci gaba da bincike.

Sanarwar ta ƙara da cewa jami’an mazaɓa da dama daga ƙananan hukumomin Musawa, Malumfashi, Matazu, Faskari da Funtua ne ake tuhuma, inda aka gano cewa sun karɓi kuɗi daga naira dubu 52 zuwa sama da miliyan 25 ba bisa ka’ida ba.

Hukumar na kuma bincikar manyan malamai huɗu na sakandare a Danja, Rimaye, Maigora da Kurami bisa zargin ɓatar da kuɗin makaranta har naira miliyan 6.6.

Ɗaya daga cikin su ma ana tuhumarsa da sayar da dukiyar makaranta da aka kiyasta ta kai daruruwan miliyoyin naira.

A wani lamari daban, hukumar ta bayyana cewa ana ci gaba da kwato kuɗaɗe daga Ma’aikatar Banki da Kudi ta jihar, inda aka yi zargin karkatar da naira miliyan 136.1.

Kawo yanzu an kwato naira miliyan 70.3, sai kuma sama da miliyan 34 da ake bi.

Sakataren hukumar, Dakta Jamilu M. Abdulsalam, ya jaddada cewa hukumar ta kuduri aniyar ci gaba da tabbatar da gaskiya da adalci, tare da kira ga jama’a da su rika bayar da rahoton cin hanci, almundahana da kuma hana amfani da ofishi ba bisa doka ba.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here