Za mu dakatar da Sufurin Jirgin sama a Najeriya daga ranar Litinin-AON

IMG 20220507 WA0003
IMG 20220507 WA0003

Kungiyar kamfanonin sufurin jiragen sama na Najeriya (AON) ta sanar cewa mambobinta za su dakatar da ayyukansu daga ranar Litinin mai zuwa saboda tsadar da farashin man fetur, wanda ya kai Naira 700 ga kowace lita.

Masu kamfanonin sun sanar da haka ne cikin wata wasika da shugaban kungiyarsu Alhaji Abdulmunaf Yunusa Sarina ya aika wa ministan sufurin sama Sanata Hadi Sirika.

Sakon da ke cikin wasikar ya sami amincewar dukkan shugabannin kamfanonin sufurin jiragen sama na kasar.
“Farashin man da muke amfani da shi na JetA1 ya tashi daga Naira 90 ga kowace lita guda zuwa Naira 700 a yanzu.

“Babu kamfanin sufurin sama da zai iya daukan irin wannan tashin farashin man a kankanin lokaci”

“Saboda haka ne muka rika tattaunawa da gwamnatin tarayya da majalisar tarayya da kamfanin mai na kasa NNPC da kuma dillalan man fetur da zummar sauko da farashin man, matsalar da ta sa tikitin tafiyar da ba ta wuce sa’a guda ba ya kai naira 120,000.” Inji Sarina.

Kazalika sanarwar ta ce: “kungiyar mu na sanar da jama’a cewa mambobinmu za su daina jigilar fasinja daga ranar Litinin 9 ga watan Mayu 2022 har illa ma sha Allahu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here