Yanzu-Yanzu: Majalisar Dattawa ta tabbatar da Farfesa Amupitan a matsayin shugaban hukumar Zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC)

Joash Ojo Amupitan 750x430 (2)

Majalisar dattawa ta tabbatar da nadin Farfesa Joash Ojo Amupitan, lauya mai lambar ƙwarewa ta (SAN), a matsayin sabon shugaban hukumar Zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC).

Wannan tabbaci ya biyo bayan zaman tantancewa da aka gudanar a babban zauren majalisar a ranar Alhamis, inda ‘yan majalisar suka yi masa tambayoyi na tsawon sa’o’i uku.

Bayan kammala zaman, shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya tambayi ko majalisar ta amince da nadin, kuma mafi yawan ‘yan majalisar suka nuna amincewa, babu wanda ya nuna adawa.

Akpabio ya yaba da amincewar tare da kira ga sabon shugaban hukumar da ya tabbatar da gudanar da zaɓe cin gaskiya tare da tabbatar da an ƙirga kuri’u da gaskiya.

A yayin amsa tambayoyi daga ‘yan majalisar, Amupitan ya bayyana cewa bai taɓa zama lauya ga jam’iyyar (APC) ba a lokacin shari’ar zaɓen shugaban ƙasa na 2023, yana mai cewa duk takardun shari’ar suna nan a bayyane don kowa ya gani.

Ya kuma yi alkawarin cewa bayan tabbatar da shi, zai tabbatar da gudanar da zaɓe cikin gaskiya da sahihanci, inda za a kai matsayin da waɗanda suka sha kaye za su rika taya masu nasara murna domin ci gaban ƙasa.

Haka kuma ya bayyana shirin inganta tsarin jigilar kayan aikin hukumar da kuma fadada ilimantar da masu zaɓe a ƙasar.

A farkon zaman, majalisar ta amince a shigar da shi cikin babban ɗakin majalisa da misalin ƙarfe 12:50 na rana bayan ƙudurin da Sanata Opeyemi Bamidele, jagoran majalisar, ya gabatar, tare da goyon bayan Sanata Abba Moro, jagoran ‘yan adawa.

Shugaban majalisar dattawa, Akpabio, ya sanar da cewa an tabbatar da amincewar Amupitan daga ofishin mai ba da shawara kan harkokin tsaro na ƙasa (NSA), hukumar tsaron farin kaya (DSS), da ofishin Sufeton ƴan sanda na ƙasa (IGP), bayan binciken bayanai da na yatsunsa.

Shugaban ƙasa Bola Tinubu ne ya aike da wasiƙar neman tabbatar da nadin Amupitan a ranar Talata, bisa tanadin sashe na 154, sakin layi na 1 na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 da aka yi wa gyara, inda ya bukaci majalisar dattawa da ta ba da amincewa cikin gaggawa.

Sabon shugaban hukumar Zaɓe mai zaman kanta ta Ƙasa (INEC) zai maye gurbin wanda ya kammala wa’adinsa, domin ci gaba da kula da harkokin zaɓe a duk faɗin ƙasar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here