’Yan ta’adda sun sake yin barazanar kai hari a Jihar Neja yayin da gwamnati ke kira da a kwantar da hankali

Bandits 750x430

Al’ummomi da dama a ƙananan hukumomin Agwara da Borgu na Jihar Neja na barin gidajensu sakamakon fargabar sake kai hare-hare, bayan ’yan ta’adda sun fitar da sabuwar barazana biyo bayan kisan gilla da ya yi sanadin mutuwar fiye da mutane arba’in a ƙarshen makon da ya gabata.

Rahotanni daga mazauna yankin sun nuna cewa ’yan ta’addan sun sanar da niyyarsu ta ci gaba da kashe-kashe, lamarin da ya jefa al’ummomin kan iyaka tsakanin Agwara, Borgu da Jihar Kebbi cikin tashin hankali da ƙauracewa gidaje.

Mazauna yankin sun kuma nuna damuwa kan yadda sojojin da aka tura yankin suka janye ba da jimawa ba bayan isowarsu, lamarin da ya bar al’ummomin ba tare da isasshen tsaro a fili ba.

Kasuwan Daji, wani ƙauye da ke kan iyakar Agwara da Borgu, shi ne cibiyar harin da aka kai a ranar Asabar, inda aka lalata ƙauyen gaba ɗaya, aka ɗaure hannuwan mutane sannan aka kashe mutum arba’in da biyu tare da ƙona gidaje da rumfunan kasuwa.

Bayanai sun nuna cewa ’yan ta’addan sun rika kai hare-hare daga maɓoyarsu da ke cikin dajin Borgu, suna wucewa ta tsaunukan Kanu da ƙauyukan Sokonbora, Bako-Mission da Shafaci, sannan suka kutsa zuwa wasu yankuna a Jihar Kebbi inda suka kashe wasu mutane tare da lalata dukiyoyi.

Hare-haren sun kuma shafi cibiyoyin addini da na tsaro, inda aka lalata wani ofishin ’yan sanda da makarantar mishan ta Katolika, tare da sace babura da wasu kayayyaki, yayin da mata da yara da dama suka faɗa hannun masu garkuwa.

Gwamnatin Jihar Neja ta tabbatar da aukuwar hare-haren tare da bayyana alhini, ta kuma nuna cewa tana aiki tare da gwamnatIn tarayya da hukumomin tsaro domin hana sake aukuwar irin waɗannan hare-hare, tare da kiran jama’a da su kwantar da hankalinsu tare da kasancewa cikin shiri da lura.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here