Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta jaddada cewa babu wani umarnin kotu da ya hana ta aiwatar da dokar hana izinin amfani da baƙin gilashin mota, duk da rade-radin da ke yawo a kai.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan Nijeriya CSP Benjamin Hundeyin ya bayyana a Abuja cewa umarnin kotun da ake ta ambato ba ya hana aiwatar da dokar, sai dai yana nufin a ci gaba da tsayawa ahalin da ake ciki a wancan lokaci.
Ya bayyana cewa a lokacin da kotun ta bayar da wannan umarni, halin da ake ciki shi ne ana aiwatar da dokar hana izinin amfani da baƙin gilashin mota, ba wai ana shirin fara aiwatar da ita ba, don haka babu wani umarni da ya dakatar da rundunar daga ci gaba da aiki da dokar.
Karin labari: Ƴan sanda za su ci gaba da aiwatar da dokar lasisin baƙin gilashin mota
Ya ƙara da cewa babban sufeton ‘yan sandan Nijeriya Kayode Egbetokun ya yanke shawarar dakatar da aiwatar da dokar ne bayan ganawa da wata tawaga daga ƙungiyar lauyoyin Nijeriya NBA, domin nuna kulawa da sauraron koke-koken jama’a.
Rundunar ta bayyana cewa dakatarwar da aka yi a wancan lokaci ba bisa umarnin kotu ba ce, sai dai domin bai wa ‘yan ƙasa damar daidaita takardunsu tare da jira sakamakon shari’ar da ke gaban kotu, amma ba a saka wa dakatarwar wani takamaiman lokaci ba.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ya nuna cewa shari’ar ta daɗe ba tare da kammalawa ba, yayin da masu aikata laifuka ke amfani da motoci masu baƙin gilashi wajen aikata manyan laifuka kamar fashi da makami da sace mutane.
Ya kawo misali na wani lamari da ya faru a jihar Edo inda wasu da ke cikin mota kirar Lexus mai baƙi. gilashi suka buɗe wuta kan ‘yan sanda yayin da ake ƙoƙarin tsayar da su, lamarin da ya yi sanadin mutuwar wani jami’i nan take, abin da ya nuna irin barazanar tsaro da motoci masu baƙin gilashi ke haifarwa.
Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da aiwatar da dokar hana izinin amfani da baƙin gilashin mota har sai kotu ta yanke hukunci a fili kan shari’ar.
NAN













































